An gudanar da wani taron manyan jami’ai domin tattauna dabarun kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, a fannin bunkasa masana’antun Afirka, ta yadda za su rika amfani da makamashi mai tsafta kuma mai dorewa.
Taron na jiya Alhamis, ya gudana ne a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, bisa jigon “Goyon bayan Sin ga inganta masana’antun Afirka: Ingiza amfani da makamashi mai tsafta, tsarawa da wanzar da ci gaba”. Kazalika, taron ya hallara kwararru, da masu tsara manufofi daga Sin da sassan nahiyar Afirka, da ma wakilai daga kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da hukumomin MDD, da masana da malamai.
Yayin taro, shugaban tawagar kasar Sin a AU Jiang Feng, ya yi bitar irin ci gaban baya bayan nan da nahiyar Afirka ta samu a fannin bunkasa masana’antu, kamar yadda matakin fara aiki da yarjejeniyar yankin cinikayya cikin ‘yanci na Afirka, da tsare-tsaren bunkasa kasashen nahiyar ya shaida hakan.
A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar.
Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan)














