A jiya Alhamis 21 ga watan nan ne aka gudanar da dandalin Legas, ko “LAGOS FORUM 2024” karo na farko cikin nasara. Dandalin ya gudana ne a jihar Legas ta kudancin Najeriya, karkashin hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake Legas, da cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya, da mujallar Najeriya mai fashin baki game da harkon tattalin arzikin Afirka da Sin, da cibiyar binciken harkokin Afirka dake jami’ar Zhejiang Normal.
Taken taron shi ne “Gudummawar Sin ga bunkasar tattalin arzikin Najeriya da zurfafa ci gaban hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya: Gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama, da samar da duniya mai karin walwala”.
- Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Hadin Gwiwa A Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD
- Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Ga Taron Kwamitin Kare Hakkin Bil Adama Na MDD Kan Hakkin Yara
Da take tsokaci yayin taron, babbar jami’ar ofishin jakadancin Sin dake Legas Yan Yuqing, cewa ta yi Sin da Najeriya na da dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, kuma musaya tsakanin su, na alamta yadda ake ingiza manufar tasirin sassa daban daban na duniya bisa tsari da daidaito.
Yan ta kara da cewa, Najeriya ta zamo magwajin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. A daya hannun kuma, zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, na da matukar muhimmanci ga aniyar ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya.
Yayin taron, masana daga Najeriya, da ‘yan kasuwa, da wakilan kafofin watsa labarai, sun tattauna game da alakar Sin da Najeriya, da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da hadin gwiwar Sin da Najeriya ta fuskar tattalin arziki na dijital da sauran batutuwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)