A kwanakin baya, kungiyar abokan hulda masu goyon bayan shawarar tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya, da kasar Sin ta gabatar, da tawagar aiwatar da shawarwarin neman ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, sun gudanar da taron tattauna manufofinsu a karon farko, a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka, inda mataimakin babban wakilin Sin a MDD, Geng Shuang, da mataimakin sakatare janar na majalisar, Navid Hanif, suka gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Geng Shuang ya ce, cikin fiye da shekaru 3 da suka gabata, shawarar ci gaban tattalin arzikin duniya da kasar Sin ta gabatar ta zama wani ra’ayi na bai daya ga kasashen duniya, har ma ta sa an fara daukar takamaiman matakai na bai daya, lamarin da ya amfanar da dimbin kasashe masu tasowa.
- Yadda Mai Haihuwar Fari Za Ta Kula Da Kanta (4)
- Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi
A nashi bangare, Mista Navid Hanif ya ce taron da ya gudana a wannan karo ya zama wani muhimmin dandalin karfafa hadin kai, da musayar ra’ayi kan dabarun da za a iya dauka wajen taimaka wa kasashe daban daban cika burikansu na samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Ban da haka, sauran wakilan ofisoshin MDD, da na kasashe daban daban, sun yabi kasar Sin kan muhimmiyar rawar da kasar ke takawa, wajen sa kaimi ga hadin gwiwa a kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban. (Bello Wang)