Guda daga cikin dattawa a Masana’antar Kannywood, wanda ya daxe ana damawa da shi; tun daga shirin wasan dave, wasan kwaikwayo zuwa shirye-shiryen da ake aiwatarwa a halin yanzu; Kabiru Nakwango a wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyana cewa, fitowa da yake yi a matsayin malamin addini; a zahiri ba haka abin yake ba.
A hirar da Nakwangon ya yi da jaruma Hadiza Gabon, a cikin shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’; ya bayyana furodusoshin fim, a matsayin waxanda ke xora masa wannan nauyi na malanta; duba da cewa yana da ilimin addini bakin gwargwado da kuma xan fahimtar harshen larabci da ya yi.
- Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala
- Ba A Kowane Irin Matsayi Zan Iya Fitowa A Cikin Shirin Fim Ba – Isa Bello Ja
Har ila yau kuma, ya bayyana rashin alaƙa ta kusa ko ta nesa da ƙasar Kwango; kamar yadda wasu ke tsammani, hasali ma bai tava ziyartar wannan ƙasa ba; illa kawai dai ya samu wannan suna ne a lokacin yarinta da wasu abokanai da sauran mutanen arziƙi ke kiran sa da shi, duk da cewa asalin sunan ba nasa ba ne.
Da yake amsa tambayoyi a kan yadda tarbiyar jaruman Kannywood, musamman mata a lokacin da da yanzu take, Nakwango ya yi nuni da cewa; abin ba a cewa komai, sakamakon yadda a halin yanzu abubuwan suka yi muni sosai; ta yadda wasu ke xaukar shigar banza a matsayin burgewa.
Daga ƙarshe, ya bayar da shawara ga masu xaukar nauyin fina-finan Hausa a halin yanzu; da su tabbatar suna yin amfani da asalin halayya da al’adun Bahaushe, ba kawai su riƙa amfani da harshen Hausa suna aiwatar da abin da ko kaxan ba halayya ko al’adar Bahaushe ba ce