An yi taron kara wa juna sani kan kare hakkokin dan Adam tsakanin Sin da Afirka ta Kudu na shekara ta 2025 a jiya Alhamis 4 ga watan Disamba a Pretoria, fadar mulkin Afirka ta Kudu. Taken taron shi ne “cimma burin karuwar mu’amalar mabambantan bangarori da tabbatar da hakkin samun ci gaba”, inda mahalarta suka tattauna kan batutuwa da dama, ciki har da manyan shawarwari hudu da kasar Sin ta gabatar, wadanda suka shafi duk duniya, da daidaita hakkokin dan Adam na duniya, da yadda hadin-gwiwar Sin da Afirka ta Kudu zai taimaka ga tabbatar da hakkin samun ci gaba.
A cewar mahalarta taron, Sin da Afirka ta Kudu suna da matsaya daya kan tsayawa ga ra’ayin mu’amalar mabambantan sassa, da samar da ci gaba tare. Kana, a matsayinsu na muhimman kasashe masu tasowa, suna da ra’ayi kusan iri daya kan batun kare hakkokin dan Adam, don haka, ya dace su kara yin cudanya da koyi da juna a wannan bangare, da aiwatar da manyan shawarwari guda hudu da Sin ta gabatar wadanda suka shafi inganta harkokin duniya baki daya, a wani kokari na bayar da gudummawa ga kare hakkokin dan Adam ta hanyar da ta dace.
Gidauniyar kare hakkokin dan Adam ta kasar Sin ko kuma CFHRD a takaice, da cibiyar nazarin Afirka da Sin ta jami’ar Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu ne suka dauki nauyin shirya taron, wanda ya samu halartar kwararru da masana da wakilai sama da 50 daga kungiyoyi, da rukunonin kwararru, da kamfanoni, da kafafen yada labarai da sauransu na kasashen biyu. (Murtala Zhang)














