An yi taron musamman na Rasha bisa taken “Kirkire, bude kofa da more Ci Gaba” a ran 27 ga watan nan da muke ciki, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya shirya tare da gudanarwa a Moscow.
A cikin jawabinsa ta bidiyo, shugaban CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, an kammala cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar dake jawo hankalin duniya cikin nasara a Beijing. Taron ya sake shelar wa duniya cewa Sin za ta fadada bude kofarta ga duniya, ta kuma bude sabon babi na samun wadata ta hanyar hadin gwiwa. CMG zai ci gaba da gina dandalin tattaunawa na duniya tare da abokan hulda, da aiwatar da shawarwarin duniya 4 da shugaban kasar ya gabatar, da kuma more shiri irin kasar na Sin a bangaren inganta tsarin shugabancin duniya. CMG zai kuma ci gaba da ba da labarin Sin mai kyau ga duniya ta hanyar amfani da karfinta wajen yada labarai, da bayyana damammakin da Sin ke samarwa a duniya.
Bugu da kari, a ranar 27 ga Oktoba, an gudanar da taron musamman na Bahrain a babban birninta Manama, da kuma taron musamman na Hungary a Budapest, duka a kan taken “Kirkire da bude kofa da more Ci Gaba”. (Amina Xu)














