Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.
Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin Asiya da Pasifik, don haka ya dace mu ba da labaran hadin gwiwa tare, mu kirkira, kuma mu bunkasa musayar al’adu, mu shiga tattaunawa da hadin gwiwa, sannan mu ba da gudummawar hikimomi da karfinmu, wajen kyautata tsarin shugabancin duniya”. (Safiyah Ma)














