Babbar kotun Jihar Kebbi, mai lamba shida a karkashin jagorancin Mai shari’a Maryam Abubakar- Kaoje, ta yanke wa wani matashi mai suna Jamilu Abdullahi da ke kauyen Dan-Warai a Karamar Hukumar Aliero hukuncin daurin rai da rai kan yi wa wata yarinya ‘yar shekara takwas da haihuwa a duniya fyade wanda yarinyar kurma ce.
Lauyan masu shigar da kara, Barista Zainab Jabbo, a nata jawabin, ta ce wanda ake tuhumar mai shekaru 13 yana fuskantar tuhuma guda daya ne kan aikata laifin fyade.
- ‘Yan Fashi Sun Kashe Wani Dan Kasuwa A Bayelsa
- Wasu A NNPC Ba Su So Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Kare – Sarki Sanusi
Ya aikata laifin ne a ranar 19 ga Watan Junairun 2023 a kauyen Dan-Warai da ke karamar hukumar Aliero a jihar.
“Wadda ta roki kotun da ta yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin da ya kama ta bisa dokar da ake tuhumarsa a kai, wanda ya yaudare ta zuwa wani gini da ba a kammala ba, inda ya yi mata fyade ta hanyar sanya zakarinsa cikin farginta ba tare da yardata ba,” in ji ta.
Barista Zainab Jabbo ta roki kotu da ta hukunta wanda ake tuhuma, saboda doka ta sanya hukuncin kan tilas.
Laifin fyaden yana da hukunci a karkashin sashe na 210 na dokar Penal Code na Jihar Kebbi na 2021.
Mai gabatar da kara ta kira da kuma gabatar da shaidu biyar, sannan ta gabatar da takardu kara shaida na tabbatar da cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin.
A nasa bangaren, lauyan da ke ba da kariya ga wanda ake tuhumar a gaban kotun, Barista Bashar Zakari, ya kira wanda ake tuhumar da ya bayar da shaida domin kare kansa a gaban kotun.
Haka kuma lauyan ya roki kotun da ta yi wa wanda ake kara adalci a lokacin da za ta yanke hukuncinta.
A cikin hukuncin kotun, Mai Shari’a Maryam Abubakar-Kaoje, ta bayyana cewa kotun ta samu wanda ake kara da laifin aikata laifin fyade.
Kotun ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da duk abubuwan da ke nuna cewa ya aikita laifin da ake tuhumarsa.
Mai shari’a Maryam Kaoje, yayin da ta bayyana laifin a matsayin “mummuna”, ta kuma bayyana cewa wanda ake tuhumar ya yi amfani da rauninta wadda aka yi wa fyaden kuma ya ci amanar yarinyar ta hanyar aikata laifin fyaden.
“Bayan an same ka da laifin da ake tuhumarka da shi a gaban wannan kotun, kotu ta yanke maka hukuncin daurin rai da rai saboda samunka da laifin lalata wata yarinya ‘yar shekara takwas da ke zaune a garin Dan-Warai a Karamar Hukumar Aliero a Jihar ta Kebbi wanda ka aikata tun a ranar 19 ga Watan Janairu shekarar 2023.
“Wannan hukuncin zai hana wasu da za su yi tunanin aikata irin wannan laifi,” in ji ta.