Rahotanni da ke fitowa game da jikin shahararren mawakin Nijeriya, Eedris Abdulkareem, sun bayyana cewa an yi masa aikin dashen koda cikin nasara.
Idan ba a manta ba shahararrun mawaka irin su M.I Abaga ne ka yi ta kira na neman tallafi yayin da daidaikun mutane a masana’antar wakar ke hada kudade don tallafa masa.
- Gwamnan Jihar Bauchi Ya Nada Sabbin Kwamishinoni 6
- An Saki Karin Ruwa Cikin Kogin Yangtze Sakamakon Fari Dake Addabar Wasu Sassan Kogin
Labarin nasarar tiyatar na zuwa ne bayan da aka yi wa Eedris dashen koda, inda matarsa ​​ta kasance wacce ta bashi gudunmawar guda.
A bayanan da danginsa ya fitar, ya nuna cewa mawakin da matarsa ​ suna samun sauki.
Mawakin wanda ya yi wakar ‘Jaga-Jaga’ ya kwanta jinya inda daga baya aka gano yana fama da ciwon koda, wanda matarsa ta sadaukar da kanta wajen ba shi guda daga ta jikinta.