ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Wa ‘Yar Shekara 2 Fyaɗe Har Ta Mutu A Bauchi

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
1 year ago
Bauchi

Wata yarinya ƙarama ‘yar shekara biyu aka samu rahoton cewa, an yi mata fyaɗe har ta rigamu gidan gaskiya, kana ya jefar da gangar jikinta a gefen wani masallaci a ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi.

A wata sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar Bauchi (PPRO) Sufuritandan Ɗansa, Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Talata, ya ce, tawagar ‘yansanda sun isa wurin da aka samu rahoton faruwar lamarin domin nemo bayanin abun da ya faru da kuma bincike.

ADVERTISEMENT
  • Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bayyana A Sakkwato
  • ’Yan Siyasar Amurka Na Bata Demokuradiyyar Kasarsu

Ya ce: “A ranar 5 ga watan Nuwamban 2024, an kai rahoton ga caji ofis ɗin ‘yansanda da ke Ningi inda aka taras da gangar jikin wata yarinya ‘yar shekara biyu amma ba ta motsi sam-sam a gefen wani masallaci da ke layin Deneva a cikin ƙaramar hukumar Ningi, sai dai alamun zargin an mata fyaɗe sun bayyana.”

LABARAI MASU NASABA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Ya yi bayanin cewa, an ɗauki gangar jikin yarinyar zuwa babban asibitin Ningi, inda a nan ne likita ya tabbatar da cewa, yarinyar ta gamu da raunuka ne sakamakon keta mata haddi da aka yi wanda har hakan ya yi ajalinta.

Kwamishinan ‘yansandan jihar CP  Muhammad Auwal Musa ya yi tir da wannan mummunar aika-aikar tare da umartar babban baturen ɗansanda (DPO) na Ningi da ya jagoranci gudanar da bincike na zahiri domin cafko masu hannu a wannan ɗanyen aikin domin tabbatar da sun fuskanci shari’a.

Kazalika, ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da suke tabbatar da kula da lafiya da tsaron ‘ya’yansu, kana suke daina barinsu suna yawo kwararo-kwararo ba tare da sanya ido ko kula ba. Kuma, ya nemi jama’a da su taimaka da dukkanin bayanin da za su kai ga cafko waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin domin ganin an ɗaɗana musu kuɗarsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Atamfar Haɗin Kan Ƙasa Da Tallafin Littafi 50,000 A Zamfara 

Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Atamfar Haɗin Kan Ƙasa Da Tallafin Littafi 50,000 A Zamfara 

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.