Al’amuran kasuwanci sun durkushe yayin da wasu fusatattun mazauna gari suka fito domin nuna rashin amincewarsu da karancin kudin sabbin takardun Naira N200, N500 da kuma N1000.
An gudanar da zanga-zangar ne a Sango-Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota a Jihar Ogun.
- Dan Shekara 14 Ya Nutse A Ruwa A Kano
- Gwamnatin Neja Ta Bayar Umarnin Kama Duk Wanda Ya Ki Karbar Tsofaffin Kudi
Mazaunan da suka je bankuna domin cire kudi sun ce ba za su iya samun kudadensu ba.
An ce sun fi tayar da hankali ne a lokacin da bankunan kasuwanci suka ki karbar tsoffin kudaden Naira don ajiye musu.
A ranar Talata, masu zanga-zangar sun tare mahadar Joju ta hanyar Idiroko zuwa Ota, lamarin da ya haifar da cikas ga masu amfani da hanyar.
A yayin da aka yi ta harbe-harbe a kan hanyar, jama’a sun yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari Allah wadai, inda suka zargi jam’iyyar APC da jefa talakawa cikin wahala.
A halin da ake ciki, an tattara ‘yansanda domin su bai wa bankuna tsaro da ma’aikatansu a Sango-Ota.
Idan za a tuna irin wannan mummunar zanga-zangar barke a Abeokuta a makon da ya gabata, inda aka kai wa bankuna hari sannan aka harbe mutum daya.