Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC.
- Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya
An bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano, da kuma digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci, inda ya ƙware a ƙirƙire-ƙirƙiren sana’o’i. Ya taɓa jagorantar ɓangaren bincike na musamman a ICPC, tare da sa aiki a fannin sa ido kan ayyukan mazabun ‘yan majalisa.
Har yanzu dai naɗin na jiran tantancewa da amincewar Majalisar dokokin Jihar Kano. A wani bangare, gwamna Abba Yusuf ya yabawa Barr. Muhuyi bisa jajircewarsa da gaskiya a lokacin da yake jagorantar hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp