Rahotanni daga ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, na cewa an kara wasu wurare hudu dake kasar Sin, cikin jerin muhimman wuraren ban ruwa na kasa da kasa ko WHIS.
Wuraren sun hada da yankin ban ruwa na tafkin Chishan, da gonaki kan tuddai na kabilar Hani na Yuanyang, da madatsar ruwa ta Jianjiangyan, da tsohon mashigin ruwa na Mentougou dake kan kogin Yongding. An ce, za a shigar da wuraren cikin sabon jerin ne a hukumance yayin taro na 76, na kwamitin zartarwar hukumar kasa da kasa mai lura da wuraren ban ruwa da magudanansu ko ICID, taron dake gudana a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Da wannan kari, adadin wuraren dake kasar Sin da aka sanya cikin jadawalin na WHIS zai karuwa zuwa 42.
Hukumar kasa da kasa mai lura da wuraren ban ruwa da magudanansu ko ICID ce ta samar da jadawalin na WHIS a shekarar 2014, a wani mataki na bayar da kariya, da kyautata ayyukan ban ruwa masu kima a tarihi, da alfanu ta fuskar binciken kimiyya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp