A ranar 10 ga watan Nuwamba da dare, an gudanar da wani bikin kide-kide a gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin domin tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar kungiyar kide-kiden Symphony ta Philadelphia ta kasar Amurka a kasar Sin. A lokacin da aka kaddamar da bikin da ya hada kide-kiden Symphony na yammacin duniya da na kasar Sin, bikin ya kasance kamar wata gadar dake sada zumunta tsakanin al’ummin Sin da Amurka.
Tun daga tarihi zuwa halin yanzu, babu dalilin lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Yayin da ake kokarin sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu, ana kuma gaggauta yin mu’amala da juna a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu. Sin da Amurka sun yi shawarwari a jere a kwanakin baya, wanda ya nuna alama mai yakini wajen tabbatar da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kana an aza tubulin ganawar shugabannin kasashen Sin da Amurka a birnin San Francisco a makon da muke ciki.
- Majalisar Ɗinkin Duniya Da Tarayyar Turai Sun Miƙa Cibiyar Kula Da Matan Da Aka Ci Zarafinsu Ga Jihar Sokoto
- Kade-Kaden Symphony Ta Philadelphia Na Ba Da Gudummawa Waje Inganta Abokantakar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
Wannan ganawa za ta kasance kamar karo na farko da shugabannin kasashen biyu za su gana da juna kai tsaye bayan ganawar da suka yi a Bali na kasar Indonesiya a shekarar bara. A yayin ganawar, bangarorin biyu za su yi musayar ra’ayoyi a fannonin tsare-tsaren raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a dukkan fannoni, da sauran manyan batutuwan dake shafar zaman lafiya da bunkasuwar duniyarmu baki daya.
Kasa da kasa na sa ran ganawar San Francisco za ta maida hankali kan batun yin hadin gwiwa da kuma samun sakamakon da ake fata.
Ana kuma fatan kasar Amurka za ta yi watsi da ra’ayin yin takara tsakanin manyan kasashe, da maida hankali kan moriyar kasa da ta jama’a, da kuma batutwan dake shafar duk duniya baki daya, ta nuna sahihanci da aiwatar da ayyuka yadda ya kamata a lokacin da take yin shawarwari da bangaren Sin bisa hakikanin halin da ake ciki a duk duniya. Ko za a iya kwantar da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, har ma dangantakar ta samu ingantu ko a’a, yana bukatar bangarorin biyu su kai zuciya nesa, kuma su yi kokari tare. (Zainab Zhang)