Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta samar da ruwa, da ayyukan more rayuwa a fadin jihar.
Malam Garba Yusuf, Kwamishinan Albarkatun Ruwa ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a ranar Juma’a a Kano.
- Ya Kamata A Tabbatar Da Hakkin Dan Adam Cikin Rayuwar Jama’a
- Gwamnatin Kano Ta Koka Kan Yawaitar Zubar Da Shara A Tituna A Jihar
Ya ce hare-haren ‘yan bindiga da hijirar mutane zuwa birane daga jihohin da ke makwabtaka da jihar ne ya taimaka wajen karuwar bukatar ruwa.
A cewarsa, lokacin da aka gina matatar ruwa ta Challawa, bukatar ruwa a Kano ya kai lita miliyan hudu a kowace rana, yanzu haka bukatar ta karu zuwa lita miliyan 200 a kowace rana.
“Ruwa wani bangare ne na rayuwa kamar yadda kuka sani, kuma dukkan halittu suna bukatar ruwa don su rayu, ita ma wannan ma’aikatar ita ce ke kula da aikin bayar da ruwa da kuma ba da gudummawa ga samar da abinci.
“Ya kamata mutane su fahimci cewa ruwa wani bangare ne na rayuwa wanda bai kamata a yi amfani da shi yadda ya dace; dole ne mu yi kokarin bunkasa dabi’ar gyara gurbatattun famfunan ruwa,” in ji shi.
Yusuf ya ci gaba da bayanin cewa ma’aikatar ta na da sashen ban ruwa da madatsun ruwa da ke kula da ayyukan ban ruwa da kuma bayar da gudummawar gaske wajen samar da abinci a fadin jihar.
Ya kara da cewa an kafa kwamitin da zai wayar da kan jama’a don sanin cewa ana sayar da ruwa.
“Kwamitin zai fadakar da jama’a kan muhimmancin biyan kudin ruwa domin samar da ruwa mai dorewa a fadin jihar.
“A Minjibir mun haka musu rijiya guda daya amma yanzu sun kai hudu kuma mun bude asusu inda suke ajiye kudinsu,” in ji Yusuf.