‘Yan Nijeriya daga sassa daban-daban na ci gaba da alhinin rasuwar tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya, Malam (Dakta) Adamu Fika (Wazirin Fika), wanda ya mutu yana da shekara 90 a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa dittijon ya yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci, kafin daga bisani ya rasu a tsakar dare ranar Talata a Kaduna bayan an dawo da shi daga asibitin Landan.
- Bamu Yarda Da Mulkin Wariya Ba A Falasdinu – Dakta Gumi
- Shin Wasan Kwaikwayon Na Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ta Kawo Karshe Ne?Â
An dai yi jana’izarsa a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a ranar Laraba, 25 ga Oktoba, 2023, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
An dai haifi Marigayi Malam Adamu Fika ne a garin Fika da yanzu haka take cikin Jihar Yobe a shekarar 1933, ya gudanar da ayyuka da dama a cikin rayuwarsa. Ya taba rike mukamin shugaban cibiyar shugabanci ta jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria.
Ya kuma rike shugabancin kwamitin amintattu na kungiyar dattawan Arewa ta ACF.
Shi dai Wazirin Fika ya fara karatunsa ne a kwalejin gwamnati da ke Kaduna, sannan ya garzaya zuwa kwalejin kimiyya da fasaha ta kere-kere wacce a yanzu ta koma jami’ar Ahmadu Bello.