ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Fashin Daji Na Cin Karensu Ba Babbaka A Jihar Katsina

by Muhammad
3 years ago
Katsina

Wani rahoto da BBC Hausa tawa wallafa yana cewa, Jama’a a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun ce sun shiga tsaka mai wuya sakamakon yadda ‘yan bindiga suka mamaye garuruwansu, kuma suka mayar da su tamkar bayi.

Mazauna yankin sun ce ƴan bindigar sun kwace gonakin jama’a, tare da tilasta wa mutanen garuruwan yi masu shuka da huɗa da ma sauran ayyukan gona.

  • ‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Kansila A Katsina
  • Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Fashin Daji Luguden Wuta, Sun Kashe 22 A Katsina

Yanzu haka dai jama’ar da ƴan bindigar suka mamaye a yankin ƙaramar hukumar Faskarin ta Nijeriya suna cikin ƙunci da damuwa.

ADVERTISEMENT

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa BBC cewa ƴan bindigar suna shiga ƙauyuka kuma su yi abin da suke so, kuma a lokacin da suke so.

Ya ce ‘‘A yanzu maganar da ake a cikin firamare din Kogo ƴan bindiga ne a ciki zaune, in an yi abinci a kai masu, in suka ga yarinya su ɗauka, in kuma ka yi magana su kashe ka.’’

LABARAI MASU NASABA

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

Mutumin ya ce mazauna yankin suna biyayya ne ga ƴan bindigar saboda basu da wani zaɓi na daban.

‘‘tashin farko dai suka sa aka haɗa masu kuɗi cikin yarjejeniyar da aka yi, da kuma gonakin da suka ware waɗanna ba za a noma ba, su za a nomawa. Duk lokacin noma za mu je can, mu yi masu hu mu yi masu noma, mu yi masu huɗa, su faɗa mana abin da za a noma, mu yi noma kuma idan lokacin girbi ya yi mu kwashe mu basu. Sun maida mu tamkar bayi a cikin wannan yanki, idan ka yi kaifi a hukunta ka’’

Ya ce ƙauyukna yankin da suka haɗa da Birnin Kogo da Yar-tsamiya da Kahi da Fankama da Hayin Dungu da kuma Gobirawa duk ƙarƙashin ikon ƴan bindigar suke, waɗanda ke ci gaba da murgunawa jama’a.

Dr Nasir Mu’azu, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina ya ce gwamnatin jihar ta farga da wannan lamari.

‘‘Mutane a irin waɗannan ƙauyuka sun je sansanin ƴan gudun hijira, to kuma wasu da yawa ba za su iya haƙuri da zaman sansanin ba don haka sai suka koma ƙauyukan su, suna ci gaba da zama bisa ga yadda ƴan bindigar suke ta gallaza masu’’

Dr Nasir ya ce gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda yana aiki tuƙuru don kula da mutanen da matsalar tsaron ta tilasta masu yin hijira da kuma tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta lashi takobin magance matsalar tsaro da ta dabaibaye garuruwa da ƙauyuka da dama na jihar. Kuma ko a kwanan nan sai da ta ƙaddamar da rundunar sintiri ta farar hula don taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

Katsina
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Cikin Shekaru 28, Kudiri Ƙasa Da 10 Sanatocin Zamfara Ta Arewa Suka Gabatar A Majalisa – Shinkafi
  • Muhammad
    2027: NNPP Ta Yi Wa Korarrun Mambobinta Afuwa, Ta Yi Alƙawarin Basu Tikitin Kai-tsaye
  • Muhammad
    Musulunci Na Fuskantar Barazana A Karƙashin Mulkin Tinubu — Datti Baba-Ahmed
  • Muhammad
    Kwankwaso Tamkar Tsuntsu Ne A Siyasa Da Yake Sauya Sheƙa Daga Nan Zuwa Can – Ganduje

MASU ALAKA

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya
Labarai

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
Labarai

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Next Post
Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Minista

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa - Minista

LABARAI MASU NASABA

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.