Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yana ci gaba da fuskantar matsinlamba kan kalamunsa game da dan takarar shugaban kasa da ‘yan arewa za su zaba a 2023.
Sai dai jam’iyyar APC da dan takarar shugabanta, Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan Nijeriya na ci gaba da mayar da martani kan kalamun da Atiku ya yi a gaban dattawan arewa da ya gudana a Kaduna a ranar Asabar da ta gabata, inda ya kada baki ya ce ‘yan arewa ba sa bukatar shugaban kasa Bayarbe ko Ibo. A cewarsa, ‘yan arewa suna bukatar shugaban kasa da ya fito daga arewa.
Da yake mayar da martani dangane da kalamun Atiku, Tinubu ya bayyana cewa bai kamata tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi magana kan shugaban kasa da ‘yan arewa za su zaba ba, inda ya ce irin wannan kalamai za su iya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Nijeriya tare da janyo kiyayya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin masu magana da yawunsa guda biyu wadanda suka hada da Cif Femi Fani-Kayode da kuma Bayo Onanuga.
Fani-Kayode wanda ya kasance tsohon ministan jiragen sama wanda a yanzu shi ne darakta yada labarai na musamman a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu/Shettima, ya ce abun da ‘yan Nijeriya kawai suke bukata shi ne, shugaban kasan Nijeriya ba wai shugaban arewa ba.
A bayanin da ya yi a garin Abuja, Fani-Kayode ya ce Atiku yana kokarin yin amfani da yanki, kabilanci da kuma addini.
Ya ce, “Nijeriya na bukatar ci gaba ne kadai. Kasarmu ba za ta taba amincewa da bambancin kabila ko yanki wajen zaben shugaban kasa ba. Atiku ya yi wannan magana ne a makance saboda yana gaban dimbin magoya bayan PDP.
“Nijeriya ba ta bukatar shugaban kasa dan arewa ko dan kudu, muna bukatar samun jajirtaccen shugaban kasa kamar Bola Ahmed Tinubu.”
Fani-Kayode ya kara da cewa mafi yawancin ‘yan arewa ba sa tare da Atiku wajen bambanta tsakanin arewa da kudu, domin duka daya suke. Ya ce ba za su taba barin Atiku ya yi mana irin cin amanan da ya yi wa Wike ba.
A nasa bangaren, daktan yada labaran na kawamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu-Shettima, Bayo Onanuga ya bayyana cewa Atiku ya nuna akidarsa karara na kokarin amfani da kabilanci da yanki wanda bai kamata ya kasance haka ba a matsayinsa na tsohon shugaban kasan Nijeriya.
Onanuga ya ce, “Wannan ya nuna yadda mutumin da ya taba rike mukami na biyu a Nijeriya kuma yanzu yake kokarin a zabe shi a matsayin shugaban kasa ya rika irin wannan kalamai marasa dadin ji.
“Ya tabbata cewa Atiku idan ya samu shugabancin Nijeriya zai rarraba kawunan ‘yan Nijeriya wanda kuma hakan bai kamata ba. A yanzu haka ‘yan Nijeriya sun san wanda ya dace su zabe a matsayin shugaban kasa ba mai kokarin kawo rabuwar kai ba a tsakanin ‘yan kasa.
“Ya kamata ‘yan Nijeriya su yi watsi da Atiku a zaben da za a gudanar a watan Fabrairun 2023, domin kasarmu tana bukatar samun hadin kai ne ba rarrabuwar kawuna ba.”
A bangaren shugabancin APC kuwa, sun bayyana cewa Atiku zai wargaza hadin kan Nijeriya da kawo rudani a zaben shugaban kasa a 2023.
A cikin bayanan sakataren jam’iyyar APC na kasa, Felid Morka, ya bayyana cewa kalamun Atiku na iya tarwatsa hadin kan kasa.
Morka ya ce, “Wannan kalamai na Atiku farmaki ne ga hadin kan kasa. Bai kamata wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasan Nijeriya a same shi yana furta irin wadannan kalamai da za su iya tarwatsa hadin kan Nijeriya domin neman samun bukatun kansa.
“Amma mu ba mu yi mamakin hakan ba domin ya nuna gazawarsa a fili na rashin iya rike mukamin shugaban kasa. Idan Atiku yana tunanin ‘yan arewa na bukatan shugaban kasa daga arewa bayan dan arewa ya kammala wa’adin mulkinsa, to yaushe ne ba a bukatar shugaban kasa dan arewa? Abin da Atiku yake tunani shi matanen kudu suke bukata a kudu.
Me ya sa ba zai yi tunanin abin da Nijeriya ke bukata ba?
“’Yan Nijeriya suna bukatar shugabanci mai ingance da zai kawo samun hadin kai a tsakanin kabilu da kuma sauran yankunan Nijeriya gaba daya. Tabbas Atiku bai cancanci zama shugaban kasa ba, domin ba zai iya gudanar da aikin hada kan ‘yan Nijeriya ba.
A yanzu kasarmu ba ta bukatar irin wadannan kalamai.”
Jam’iyyar APC ta kara da cewa wannan kalamu na Atiku su ne masu ruguza kasa cikin gaggawa maimakon samun hadin kan kasa da Nijeriya ke bukata.
Shi ma a nasa bangaren, tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Kingsley Moghalu ya bukaci Atiku ya nemi afuwan ‘yan Nijeriya.
Moghalu wanda ya yi magana a shafinsa na Tuwita da ya bayyana cewa ya yi matukar rashin jin dadinsa dangane da kalamun tsohon mataimakin shugaban kasa wanda har yanzu yana girmama shi.
Mataimaki na musamman kan yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Louis Odion ya bayyana cewa kalamun Atiku na iya lalata hadin kan Nijeriya gaba daya.