Hukumomi a kasar Masar sun ce mutum 16 sun bace, ciki har da ‘yan kasashen waje, sannan an ceto 28 bayan wani jirgin ruwan ‘yan yawon bude ido ya nutse a tekun Bahar Maliya.
Hudu daga cikin wadanda ake neman ‘yan Masar ne yayin da sauran sha biyun yan kasashen waje ne, ciki har da masu yawon bude ido ‘yan kasar Finland da Birtaniya.
- Gidauniyar Buratai Ta Taya Giwa-Daramola Murnar Zama Shugaban Kungiyar Tseren Kwale-kwale Na Ondo
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Kaddamar Da Jirgin Ruwa Mai Aikin Nazari A Teku Mai Zurfi
Wakiliyar BBC ta ce hukumomin Masar sun ce mutum 44 ne cikin jirgin, sha uku daga ciki ma’aikatan jirgin ne yayin da sauran talatin da daya masu yawon bude ido ne.
Hukumomin kasar ba su bayyana dalilin da ya haddasa nutserwar jirgin ba, sai dai bayanai daga wadanda suka tsira sun nuna cewa igiyar ruwa ce ta afkawa jirgin da ya yi sanadin kifewarsa.
Masu hasashen yanayi sun yi gargadi game da tafiya kan teku a ranar Lahadi da Litinin.