Mambobin jam’iyyar APC da suka hada da shugabanninta da sauran masu fada aji na jam’iyyar sun fara kai ruwa rana,hakan ta faru ne sanadiyar yadda ake son ayi karba- karba da mukaman wadanda za su shugabanci majalisun biyu, na Dattawa da Wakilai na majalisa ta goma da za a kaddamar a watan Yuni.
Duk da yake kwamitin zartarwa na jam’iyyar bai ce komai ba dangane da matakin da zai dauka kan sassan da za su samu shugabancin majalisun manufa inda za a kai su, Jaridar LEADERSHIP ta bada rahoton cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun shirya tsaf kowa ya ja daga sai na shi bangaren, musamman ma idan mukaman Shugaban majalisar dattawa dana Wakilai ba a kai su sashen su ba.
- Nijeriya Ta Sanya Hannu A Yarjejeniyar Amfani Da Fasahar Shuka Itatuwa Da Kasar Netherlands
- Yawan Hatsi A Kasar Sin Zai Ci Gaba Da Karuwa A Bana
Kodayake dai an samu hakikanin bayani mai gamsarwa al’amarin neman Shugabancin majalisun biyu da za a kaddamar watan Yuni, kowa yana iya nema daga sassa shida na Nijeriya, mabobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar suma sun daura zare kowa yana kallon na shi sashen,dangane su wanene za su kasance shugabannin su.
Amma wasu dafa cikin shugabannin jam’iyyar sun tsaya kai da fata na cewa tunda yake Shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima duk musulmai ne, idan har ana son ayi ma Kiristoci adalci ya dace a bar masu Shugaban majalisar dattawa dana majalisar Wakilai ta kasa.
Wasu daga cikin mambobin jam’iyyar da suke musulmai suna matukar nema ruwa a jallo su zama Shugaban majalisar dattawa da Kakakin majalisar wakilai ta kasa.
Daga sashen Arewa maso yamma akwai Sanatoci kamar Jibrin Barau dan majalisar dattawa ta (Kano ta Arewa ) da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari dan majalisar dattawa (Zamfara ta yamma), suma suna ta kai gwauro da mari daya daga cikinsu ya kasance Shugaban majalisar dattawa.
Hakanan ma akwai Sanata mai wakiltar majalisar dattaawa ta Neja ta gabas, Sani Musa, daga Arewa ta tsakiya shi ma ya sha alwashin sai ya zama Shugaban majalisar dattawa.
Daga Kudu maso kudu tsohon Ministan harkokin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio, da aka zabe shi a majalisar daga wancan sashen.
Daga sashen Kudu maso gabas akwai tsawatarwa na ‘yan majalisar dattawa Sanata Orji Uzor Kalu; gwamanan Jihar Ibonyi Ebonyi Dabe Umahi,da aka zaba lokacin zaben Shugaban kasa dana ‘yan majalisar kasa da aka yi 25 Fabrairu ya wakilci mazabar majalisar dattawa ta Ebonyi ta Kudu, ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa.
Maganar Kakakin majalisa ko shugabanta na majalisar Wakilai ta kasa an samu labarin dake nuna matakin da wani dantakara ya dauka domin ya karya lagon wata ka’idar da ake son abi, an samu labarin daya daga cikin ‘yan takarar da ake kira da suna Betara yana son yin takarar kamar yadda aka yi bayani ba wata karba-karbar da ake son yi. Matakin na shi ya sa mataimakin Shugaban kasa mai jiran gado Kashim Shetima da gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum abin bai masu dadi ba.
Dukkansu kamar yadda aka samu labari basu dadin yadda Betara ya nuna sha’awarsa ta shugabancin majalisar ba.
Aboki shakikin Betara wakilin jam’iyyar NNPP daga Jihar Kano, Abdulmumini Jibrin kwanaki uku da suka wuce ya fadawa ‘yan jarida cewar shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Wakilai hannun shi bude yake abinda zai sa ya samu nasara ke nan koda kuwa ace jam’iyyar APC ta hana sashen Arewa maso gabas daga neman shugabancin majalisar.
Bayan Jibrin akwai wani dan majalisa da yayi wa’adi na biyu daya fada ma wakilinmu cikin yarda cewa dan majalisa daga Jihar Borno ya kasance mai sayar da zuma gina aka samu shi ba sai yayi talla ba, mai madi ne ke talla.
“Wani abu daban da akwai wani hasashe dawasu suke yi domin duk da mataimakin Shugaban kasa mai jiran gado da gwamnan Borno sun sha alwashin sai sun taka ma Betara burki.
“Mun san su ba Allah bane suna dai jin tsoron Betara ne domin yana da farinm jinin jama’a ta haka kuma yana iya kwace duk abinda suke ganin suna takama da shi daga gare su da zarar ya zama Shugaban majalisar wakilai” ,kamar dau yadda wani dan majalisa daga Kudu maso yama yace.
Sai dai ba bar garin ba sai ga Kura saboda kuwa akwai wasu gamaiyar masu fada aji na APC da ke kiran kansu da sunan Integrity Caucus (AIC) ko masu son a rika kamnta gaskiya a majalisa da masu harkoki sun daga da cewa dole ne sai sashen Arewa maso yama ne zai bada Shugaban majalisar dattawa ta goma.
Su masu fada aji daga Arewa maso yamma sun yi wannan tunanin ne a wani abu da suka ce wani shiri na jam’iyyun adawa su mamaye Kano da gaba dayan ‘yan majalisar APC daga shiyyar
Da suke ganawa da manema labarai a Abuja masu ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu kan kiraye- kirayen da mambobi daga jam’iyyun adawa su keyi bama kamar (NNPP)kada Shugabannin jam’iyyar APC su kai mukamin Shugaban majalisar dattawa zuwa sashen Arewa maso yamma.
Kamar yadda has ashen su ya nuna wani shiri ne da ake yi na hana shi sashen wani babban mukamin gwamnti, domin hakan na iya basu damar fadada yawansu daga karshe ma suna iya kwace Kano ko gaba daya ma sashen na Arewa maso yamma a shekarar 2027.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ta AIC, Honorabul Musa Ahmed Jauro Dutse,da ya yi magana da manema labarai a madadin ta yace,jam’iyyun adawa suna guna- guni ne fiye da yadda ya dace su yi,kan maganar karba- karba kawai domin su rikita Shugaban kasa mai jiran gado Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,da sauran Shugabannin APC ta bar masu sashen Arewa maso yamma.
Dutse ya ce: “Duk mun gane manakisar tasu duk suna yin haka ne don hana sashen neman mukamin Shugaban majalisar dattawa ba don komai ba don ra’ayin su na hana sashen samun wani babban ofis a karkashin gwamnati mai shirin kama mulki nan bada dadewa ba.Shi yasa muke nuna masu mun gane duk take- taken nasu.
“Sashen Arewa maso yamma shi yafi bada kuru’in da suka fi na ko wane sashe yawa lokacin zaben Shugaban kasa don haka ya dace ayi adalci da kamanta gaskiya ayi ma shi sashen abinda yakamata domin gudunmawar da ya bayar lokacin zaben.
“Maimakon haka ma mun gane duk take – taken su bai wuce na kokarin su gina ma APC ramin mugunta wanda za ta zurma domin mai zurfi ne ta fada a shekarar 2027 da haka sun kwace sashen ke nan.Kar mu amince da su, kada mu kyale su,kar mu bar su su samu yin nasara kan kudurin nasu.Ba za a maida sashen Arewa maso yamma saniyar ware ba, maimakon haka ma kamata yayi ayi ma sashen abinda ya dace saboda yawan kuri’un da ya samar.”
Kungiyar ta tsaya kai da fata cewa tunda sashen Kudu maso yamma shi ke da Shugaban kasa, Arewa maso gabas na da mataimakinsa,adalcin daya dace shi ne Shugaban majalisar dattawa ya fito daga Arewa maso yamma.
Kungiyar ta bada cikakken goyon bayan ta ga takarar Sanata Barau Jibrin akan mukamin Shugaban majalisar dattawa na 10, domin ya dace da kuma kwarewar da yake da ita,bugu da kari duk yafi Sanatocin da suka fito daga sashen cancantar rike mukamin.
Lukman, Ndoma-Egba sun yi kira da ‘yanmajalisun Su yi ma ko wane sashe adalci
Amma mataimakin Shugaba kasa na jam’iyyar APC (Arewa maso yamma) Mallam Salihu Moh Lukman, ya ki amincewa da masu fada aji daga sashen shi dangane da karba- karba da mukamin Shugaban majalisar dattawa.
Ya ce abinda bai dace bane bama kamar sashen mulki na Nijeriya ace musulmi yana neman a zabe shi Shugaban majalisar dattawa.
Lukman ya samu goyon bayan tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Bictor Ndoma-Egba (SAN) da ya ba jam’iyyar APC shawarar ta aki mukamin Shugaban majalisar dattawa da Kakakin majalisar wakilai ta kasa zuwa sashen Kudu maso gabas da Arewa ta tsakiya.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa jiya ne yayi kira da gwamnonin APC,masu ruwa da tsaki, da duk ‘yan jam’iyyar su sa baki wajen kira ga duk wadansu musulmai masu sha’awar takara su bari.
A wani bayani daya fitar a Abuja mai taken ‘ Takarar nuna kudi wajen neman Shugabancin majalisun kasa’,Lukman yace tuni an zabi musulmai biyu da za a rantsar Shugaban kasa da mataimakinsa ranar 29 ga Mayu 2023,don haka duk wani kokarin da ake nab a wani musulmi mukamin Shugaban majalisar dattawa zai nuna yadda musulmai suka mamaye gwamnatin tarayya, abin zai iya zama wani abinda za ayi ta tsegumi,ba kuma zaio yi ma hadin kan Nijeriya dadi ba, da maganar zaman lafiya,wannan bai dace a bari al’amarin ya faru ba.
Ya nuna cewa wannan wani al’amari ne da zai iya kawo cikas wajen samun cigaba da zaman lafiya tsakanin al’ummar Nijeriya,sai dai wani abu kuma an sa ido ne ko hankali ya koma ga wanne irin matakin da Shugabannin siyasa na kasa wato Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabnta na yanzu da zai gaje shi Shugaban kasa mai jiran gado Asiwaju Bola Tinubu, zasu iya dauka kan al’amarin.
Lukman ya kira abin da ban takaici ba kuma za a amince da shi bada yake da matukar hadari saboda ai nakwai ka’idojin zabe da za abi domin zaben Shugabannin majalisa ta 10,al’amarin a barshi hakanan kara zube.
“A lokacin da jam’iyyun adawa suka kunshi masu ra’ayin addini,ko amfani da siyasa da zasu iya yin duk wata karya domin cimma burinsu.Ba zamu barsu ba su tsaya takarar Shugabancin majalisa ta 10 abin ya cigaba da tafiya babu taka burki ba.
“Kamata yayi a dauki duk matakin daya dace duk wasu ruwa da tsaki,Shugabannin jam’iyya, mambobin da aka zaba,da suke son a zabe su mukaman shugabanci na majalisa ta10,kowa ya san abinda yake yi da kuma dacewa da shi.
Shi ma a nashi matsayin Ndoma-Egba ya yi kira da APC ta kai mmukamin Shugaban majalisar dattawa sashen Kudu maso gabas,yayin da Kakakin majalisar tarayya a kai shi Arewa ta tsakiya.
Ya yi kira da jam’iyyar ta tabbatar da dukkan mukaman ofisoshin an ba Kiristoci su.
Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin safe na gidan Talbijin na Arise News jiya.
Kamar yadda yace Nijeriya ta wuce da al’amarin ‘dantakara da mataimakinsa duk muslmai na Shugaban kasar da aka zaba,Tinubu yace irin wannan zaben a majalisar kasa na iya kawo rashin jituwa.
Ya ce, “Bari in fada ma akwai abubuwa uku dangane da wannan al’amarin, abu na farko shine tsarin mulki, na biyu kuma tarihi,na uku kuma shi ne yadda ake yi,idan ka bani dama bari in karanta maka kai tsaye daga tsarin ulki,saboda ina bukatar a fahimci yadda al’amarin yake.Sashi na 14 na tsarin mulkin Nijeriya na 1999 yace a karamin sashe na 1 saboda damukuradiyya da adalci “.
“ Sai dai babban al’amari shi ne karamin sashe na 3, “ yadda ake hada gwamnatin kasa da duk wadansu bangarorinta da yadda za a tafiyar da al’amuranta sun dace a tabbatar da kowane sashe ana damawa da shi,saboda a samu hadin kan al’umma,bai dace a ce wasu daga wata Jiha sumn mamaye abubuwa, ko kabila daya tayu kaka- gida,a gwamnati ko wata hukuma ba.
“Ita maganar kamar yadda take a sashei na 14 na ya kasance dukkan wadanda suka dace su kasance a tafi tare dasu saboda tabbatar da adlaci da daidaituwa.Kamar yadda yai bayani shi ne sakataren tsara kamfen na shugaban kasa.Ina nan lokacin da maganar dantakara da mataimakinsa duk musulmai.Wani babban al’amari ne wurinmu mu Kirista da ‘yan Kudu.
Ndoma-Egba ya ja kunnen mutane da cewa Nijeriya Allah yasa ta shawo kan matsalolin da suka taso dangane da dantakara da mataimakinsa duk addininsu daya na musulunci.
Ya ce “Abin yana iya shafar domin shi tsarin mulki babu abinda ya bari.Dole ne komai su kasance sunanan ko wanne sashe.Ko wane sashe, maganar addini,ko kabilanci sai an yi tafiya tare,musamman ma wajen tafiyar da gwamnati awannan kasa tamu Nijeriya.
Ya ce amfanin da yake ba taba zama shugaban masu rijaye na majalisar dattawa, sai in tunatar da ‘yan Nijeriya tarihi da yadda ake tafiyar da Shugabancin majalisar dattawa.
“Na san cewa Osita Izunaso yana majalisar wakilai ta kasa hakanan ma majalisar dattawa lokacin da nake can, wani lokaci kafin ya bar can ya amshi mukamin sakataren tsare- tsare na kasa na jam’iyyar APC na ji labarin cewa zai dawo majalisar dattawa.Hakanan ma akwai Sanata Orji Uzor Kalu, wanda shi ma ya kasance a majalisar wakilai ta kasa na wani lokaci.
“ Ya kasance a majalisar dattawa ina ganin wannan shine karo na biyu, shi yana daga cikin masu mukamai, dukkansu kowa ya cancanta duk Sanatatoci ne amma ni bani da dantakarar dana fi so daga cikinsu.Abu mafi dacewa shi ne a bi tsari, yadda ya dace da kuma adalci kamar yadda ya ce.
Ndoma-Egba ya yi kira da duk ‘yan takarar mukaman masu maiko daga Arewa su fita daga cikin masu neman mukaman,su sadaukar da son zuciyarsu, su kalli hadin kan kasa.
Izunazo zai fafata da Kalu a sashen Kudu maso gabas.
Yanzu dai Sanata mai wakiltar mazabar majlisar dattawa ta Imo ta yamma Osita Izunaso,ya fara tuntubar mutane dangane shugabancin majalisar dattawa da yake sha’awa.
Yace shi yafi cancanta ya kasance a kujerar Shugaban majalisar dattawa shi ne kuma babban Sanata a sashen Kudu.
Izunazo ya shirya ya fafata da mai tsawatarwa ‘yan majalisa tsohon gwamnan Jihar Abia Sanata, Orji Uzo Kalu,da shi ma ya nuna sha’awarsa ta ya tsaya takarar neman shuugabancin majalisar dattawa.
Tsohon sakataren tsare- tsare na jam’iyyar APC na kasa a fdarShugaban kasa makon daya gabata ya sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan niyyar da yake ta tsayawa takarar neman shugabanci na majalisar dattawa.
Da yake ganawa da manema labarai a Abuja, Senator Isunazo yace abu mafi dacewa shine masu ruwa da tsaki ajam’iyyar said it would be proper for t APC su amince da sashen Kudu maso gabas wanda an dade ana maida shi saniyar ware.
Ya ce idan aka bar mukamin zuwa sashen nasu zai kwantar da akidar da ake da ita samun kasar Biyafara da magoya bayan kungiyar IPOB suke ta ikirarin hakan.
Ya kara jaddada cewa, “Amfanin tafiya sosai das ashen Kudu maso gabas a al’amarin siyasada maganin masu tada kayar baya wajen neman kasar Biyafarabama kamar tsakanin matasa wadanda ka dade da rudarsu bin tafin kungiyarIPOB/ESN,Bada goyon baya kan bukatar sashen Kudu maso gabas wajen neman shugabancin majalisar dattawa wannan ma zai taimaka wajen kwantar da kura.
“A siyasance abu mai kyau ne a hana tasirin Peter Obi da IPOB/ESN a sashen Kudu maso gabas, hanya mafi dacewa ta cimma wannan burin ita ce wani mutum daga wancan sashen ya hau kan matsayi na uku a Nijeriya”.
Ya kara bayanin idan aka yi la’akari da kwarewar da yake da ita ta tsohon dan majalisar wakilai ta kasa kuma tsohon ma’aikacin majalisar kasa, kuma tson mamba na kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC, shi yafi dacewa a ba wannan mukamin domin zai bunkasa aiki da son juna da inganta danganta tsakanin majalisar zartarwa, ‘yan majlaisa, da kuma bangaren shari’a da kuma sakatariyar jam’iyyar APC.
Hukumomin yaki da cin hanci suna bin diddikin ‘yan takara da suke fate tare da dala
Ranar litinin ce hukumar (EFCC) ta ki yin bayani kan rahoton yadda take bin diddikin ‘yan majalisa masu sha’awar takara suke bada dala domin samun shugabancin majalisun kasa.
Wannan ya biyo bayan bayan wani zargin da aka yi na wasu ‘yan takara suna bada cin hancin yayin da maganar zaben shugabannin majalisun kasa yake kara karatowa, don haka ne su hukumomin suka kara zage damtse wajen yakin da suke yi na wadanda suke amfani da kudi domin a zabe su.
Wata majiya daga ma’aikatar shari’a ta fadawa tawagar manema labarai a Abuja ranar Litinin da darean fara daukar matakan domin kama ‘yan takara masu kashe kudade da yawa domin samun mukaman majalisa ta 10.
Wannan ya biyo bayan rahoton da aka samu mainuna cewa mataimakin Shugaban kasa mai jiran gado Kashom Shettima da gwamnan Jihar and the Borno,Babagana Umara Zulum sun sa tsare tsakaninsu da wani dan takara wanda sunansa yafi shiga zuciya Muktar Aliyu Betara.
Hukumomin (EFCC) da (ICPC) kamar yadda wani rahoto ya nuna zasu rika bibiyar ‘yan takarar bama kamar wadanda suke bakin zuwa majalisa ne musamman tarurrukan da suke yi.
Kamar yadda aka samu bayanai hukumomin sun samu tabbataccen rahoto mai nuna daya daga cikin ‘yantakara a mukamin Shugaban majalisar wakilai kowane dan majalisa a bashi dala milyan $12.5 million (kowane dan majalisa dala $50,000) kafin ayi kaddamawar ta ‘yan majalisun.
Wasu daga cikin masu takarar Shugaban majalisar Shugaban dattawa sun hada da tsohon gwamnan Jihar Abia yanzu kuma shi ne mai tsawatarwa na majalisar dattawa Dr.Orji Uzor Kalu;Sanatoci Jibrin Barau (APC,Kano ta Arewa);Sani Musa (APC, Neja ta gabas)da Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu).
Kamar yadda ake ta yamadidi akwai manyan Sanatoci daga Jihar Zamfar, Abdulaziz Yari (APC, Zamfara ta yamma);gwamna mai baring ado na Jihar,Dabid Umahi (APC, Ebonyi ta kudu)da tsohon gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole (APC, Edo North).
‘Yan takara masu neman a zabe su Shugaban majalisar wakilai ta kasa sun hada da Idris Wase daga Jihar Filato, Makki Yalleman daga Jihar Jigawa, Adamu Yusuf Gagdi daga Jihar Filato, Benjamin Kalu daga Jihar Abia, Peter Akpatason daga Jihar Edo, Muktar Aliyu Betara daga Jihar Borno , Sada Soli Jibia from Katsina State,Tunji Olawuyi daga Jihar Kwara,Abbas Tajuddeen daga Jihar Kaduna da Aminu Sani Jaji daga Jihar Zamfara.
Majiyar ta ce “ dukkan matakan da suka kamata an dauka domin a gano da bin diddiki na urinkudade masu yawa da ake kashewa kafin a kaddamar da majalisa ta 10 domin akwai tabbatattun rahotanni da ke nuanwasu ‘yan takara masu kudi, bama kamar sabon zuwa majalisa suna amfani da kudi domin jan ra’ayin wadanda za suyi zaben Shugabnnin majalisar.
“Wannan ba abu mai kyau bane ga damukuradiyyarmu kota wane bangare,mako uku da suka gabata muna ta samun rahotanni na baka da kuma rubutattu,yadda ake ta kashe kudade domin kawai asamu Shugabanci.
“Mun ma samu wani rahoton da aka aiko daga Arewacin Nijeriya dangane da wani dan majalisa mai neman a zabe shi Shugabanci majalisar wakilai. Bamu da wasu cikakkun gamsassun bayanai, amma mun kai wani lokacin da zamu dauki mataki domin duk wasu masu fada aji ta bangaren tsaro da wadanda suka dace su san abinda ake ciki akan maganar zaben Shugabannin majalisa ta 10.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp