Hukumar kulawa da al’amuren da suka shafi itatuwan shukawa ta kasa ta sanya hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin kasar Netherlands mai suna Groasis B.B da kuma kamfanin Nijeriya mai suna ‘Boplas Industries Limited Nigeria’ yarjejeniyar zai tabbatar da amfani da da fasahar zamani mai suna ‘waterbodd’ na banruwa ga shuka wanda za a yi amfani da shi wajen samar da itatuwan da ake bukata na ‘Great Green Wall’.
Yarjejeniya zai taimaka wa Nijeriya wajen aiwatar da shirinta na shuka itatuwa a yankunan da aka fi bukatar shuke-shuken a bangarorin Nijeriya.
- Tattalin Arzikin Sin Ya Kara Samar Da Dama Ga Bunkasuwar Sauran Kasashen Duniya
- An Kwaso ‘Yan Nijeriya 107 Da Suka Makale A Libya
Bayanin haka yana kunshe ne a takardar sanarwa da jami’ar watsa labarai na hukumar, Misis Pauline Sule ta raba wa manema labarai a Abuja.
Ta kara da cewa, a ranar 14 ga watan Afrilu ne aka sanya hannu a kan yarjejeniyar, wanda haka zai kara kaimin aikin da ake yina shuka itatuwa a yankuna 11 da hukumar ke kula da su.
“Fasahar ‘waterbodd’ na taimaka wa wajen tsimin ruwa yana kuma taimakawa wajen inganta rayuwar itatuwan da aka shuka yana kuma rage yawan ruwan da ake amfani da shi wajen ban ruwa ga itatuwan, tuni kasashe fiye 55 suke amfani da shi wajen shuka miliyoyin itatuwa a sassan duniya.
“A kan haka hukumar NAGGW ta nuna sha’awarta a amfani da wannan fasahar da ya samu karbuwa a sassan duniya.
“Shugaban hukumar, Dakta Yusuf Maina Bukar ya jagoranci tawagar Nijeriya wajen sanya hannun a yarjejeniyar, ya kuma yi alkawarin tabbatar da Nijeriya ta ci gajiyar dukkan amfanin da ke cikin shirin gaba daya.”