• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Fatan Amurka Za Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Bayan Ziyarar Janet L. Yellen A Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Sakatariyar baitilmalin kasar Amurka Janet L. Yellen za ta kammala ziyarar aikinta a nan kasar Sin a yau Talata. Yayin ziyarar, Sin da Amurka sun yi mu’ammala tsakanin manyan jami’ai da bangarori daban daban, inda suka amince da tabbatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare kuma da cimma daidaito wajen kara azama kan bunkasuwar tattalin arziki da yin hadin gwiwa a hada-hadar kudi. A cewar Janet L. Yellen, Amurka da Sin kamata ya yi su daidaita huldarsu ta bangaren tattalin arziki bisa nauyin dake rataye a wuyansu, tare kuma da bayyana matsayin kasar na yin watsi da ra’ayin katse hulda da Sin.

To, Janet L. Yellen ta ambaci kalmar nauyi, mene ne ainihin ma’anar sauke nauyi? Ba kawai Amurka ta sauke nauyin dake wuyanta wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikinta da mai da hankali kan muradunta kawai ba, dole ne ta kara kawo wa kamfanoni da al’ummomin kasashen biyu alheri, har ma da yin tunani kan yadda za a samu moriyar juna, da tinkarar kalubalen duniya baki daya, da ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Ta yaya za a tabbatar da wadannan abubuwa? Akwai wasu ma’aunonin da za a kimanta abin da Amurka ke gudanarwa, na farko, dakatar da siyasantar da batun tattalin arziki, kuma kada ta tada zaune tsaye bisa hujjar kiyaye tsaro, da kuma yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka bisa dokokin tattalin arziki da ka’idojin kasuwa.

  • Xi Jinping Ya Gana Da Ministan Wajen Rasha Sergey Lavro
  • Shin Kwalliya Za Ta Biya Kudin Sabulu Game Da Ziyarar Yellen A Wannan Karon?

An ruwaito cewa, Janet L. Yellen ta bayyana kin amince da ra’ayin katse hulda da Sin, yayin da take ziyara a birnin Guangzhou da Beijing. Sin na maraba da hakan sosai, tana mai fatan Amurka za ta dauki matakan a-zo-a-gani.

A bana, an cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Tarihi ya shaida cewa, muradun Sin da Amurka na da dogaro da juna. Zurfafa hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen 2 ya dace da muradunsu, kuma ya amfana wa bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. Ko Amurka za ta sauke nauyin dake wuyanta, bari mu jira. (Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
Sallah: Gwamnatin Katsina Ta Yi Wa Fursunoni 222 Afuwa

Sallah: Gwamnatin Katsina Ta Yi Wa Fursunoni 222 Afuwa

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.