An gabatar da kananan na’urorin chip na kumfyutar Quantum na kasar Sin a karon farko, yayin wani shirin bidiyo na kai tsaye na CMG a ranar Talata, wadanda za su samar da kumfyutar Quantum ta kasar Sin mai suna Wukong.
Jia Zhilong, mataimakin daraktan cibiyar binciken ayyukan injiniya da tsarin kumfyutar Quantum ta lardin Anhui, ya ce a karshen shekarar da ta gabata ne aka samar da kanana na’urorin chip na Quantum da aka sanyawa Wukong, inda a yanzu haka suke aikin tantancewa da cire kurakurai a cikin kumfyutar. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)