A yau Litinin aka bude wani taro na masu mukamin magajin gari ko wakilansu da jami’an diplomasiyya da malamai daga kasashe 10, a birnin Dunhuang dake kan hanyar Siliki a lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin.
Makasudin taron shi ne, tattauna damarmaki da kalubalen da tafiyar da ayyukan kare al’adu ke fuskanta a birane.
Yayin da ake fama da karuwar kaura zuwa birane a duniya, mahalartar taron sun jadadda muhimmancin daidaita ayyukan kare al’adu da na raya birane. Sun nanata bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a matsayin wata hanya ta tunkarar wadannan kalubale na bai daya.
A matsayin birnin dake karbar bakuncin taron, Dunhuang mazauni ne ga wurare 3 dake cikin jerin wuraren gargajiya na hukumar UNESCO da kuma wuraren kayayyakin gargajiya sama da 260, wanda kuma ke nuna hadaddun dabarun da aka dauka a shekarun baya-bayan nan da nufin kare al’adun gargajiya yayin da ake bunkasa birnin. (Fa’iza Mustapha)