Yanzu haka ana gudanar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, karo na 30, wato “COP 30” a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil, inda a ranar Juma’a 14 ga wata aka kira wani taro a gefe mai taken “Dabarun Kasar Sin Na Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya”, don bayar da fasahohin Sin a fannin daidaita al’amura a kokarin sabawa da sauyin yanayi.
A wajen taron, shugaban tawagar kasar Sin a taron COP30, kana mataimakin ministan muhallin halittu na kasar, Li Gao, ya ce sauyin yanayin duniya wani babban kalubale ne da daukacin bil Adama ke fuskantarsa, inda a nata bangare, kasar Sin ta tsaya kan mai da hankali kan dukkan bangarorin dakatar da sauyin yanayi, da kokarin sabawa da shi. Kana kasar tana gudanar da gwaje-gwaje a biranenta 39 ta fuskar daidaita tsare-tsare don sabawa da sauyin yanayin duniya. Ban da haka, jami’in ya ce, kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a kokarin tinkarar sauyin yanayi, da inganta fannin sabawa da sauyin yanayin duniya a kasashe daban daban.
Duk dai a wajen taron, Francesco Corvaro, wakilin kasar Italiya mai kula da batun sauyin yanayi, ya yi yabo ga kasar Sin bisa nasarorin da ta samu a kokarin sabawa da sauyin yanayin duniya, inda ya ce ci gaban da kasar Sin ta samu ya nuna makomar aikin tinkarar sauyin yanayi a duniya, kuma yana sa ran ganin Sin ta zama tamkar wata gada mai hada dukkan bangarorin kasashe masu tasowa da masu sukuni, ta yadda za a tabbatar da hadin gwiwar daukacin bil Adama a kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya. (Bello Wang)














