Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, Xinjiang za ta bude kofarta ga duniya, yana mai cewa, kasar Sin tana maraba da karin abokai daga dukkan kasashen duniya, da su ziyarci Xinjiang, don ganin yadda ake maraba da baki, da zaman jituwa da kuma wadata.
Wang Wenbin ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na yau da kullun, yayin da yake karin haske kan wani sharhi na baya-bayan nan da Moiz Farooq, babban editan jaridar Daily Ittehad Media Group ya rubuta game da ziyarar da ya kai jihar Xinjiang ta kasar Sin.
- Dalibin Kasar Benin: Ina Da Burin Kai Fasahohin Aikin Noma Na Kasar Sin Zuwa Kasar Benin
- Xi Jinping: Ya Kamata Daukar Nauyi Ya Zama Al’ada
Wang ya ce, a shekarar 2023 kadai, Xinjiang ta karbi tawaga da kungiyoyi kusan 400 wadanda suka kunshi maziyarta sama da 4,300 daga kasashen Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Uzbekistan, da Pakistan, da Indonesia. Sauran sun hada da kasashen Malaysia, da Japan, da Masar, da Faransa, da Jamus, da Switzerland, da Canada, kungiyar hada kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan Islama da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa.
Wang Wenbin ya ce, wasu daga cikinsu jami’an gwamnati ne, ko jami’an diplomasiyya, malaman addini, masana, ‘yan jarida da matafiya na yau da kullum. Inda suka ziyarci wurare da dama a jihar, sun kuma saurari malamai da suke gabatar da wa’azi a masallatai da cibiyoyin addinin Musulunci, baya ga wuraren tarihi na gargajiya da suka ziyarta don ganin yadda ake kare al’adun gargajiyar jihar. Haka kuma sun ziyarci masana’antu da wuraren kasuwanci da gonaki don ganin yadda ake nomawa da sarrafa kayayyaki a Xinjiang. Kana sun ziyarci gidajen talakawa, inda suka ga yadda al’ummomin kabilu daban daban ke rayuwa cikin farin ciki da jin dadi.
Kakakin ya ce, gani ya kori ji, mutane sun ga zahiri da idonsu.(Ibrahim)