Jiya Litinin, Donald Trump ya sanar da farawar wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban kasar Amurka a hukumance. Kafin hakan, a yayin zantawarsa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ta wayar tarho a ranar 17 ga wata, shugabannin biyu sun cimma matsaya cewa, ya kamata a sada zumunta na dogon lokaci a tsakanin Sin da Amurka, da kuma yin hadin gwiwa domin kiyaye zaman lafiyar duniya. Haka kuma, sun cimma matsaya kan manufar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, lamarin da ya samu amincewa daga bangarori daban daban.
Shin Sin da Amurka, abokan gaba ne ko abokan arziki? Wannan batu yana da nasaba da tushen tafiyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Sau da dama, kasar Sin ta sha jaddada cewa, tana son zama abokiyar arziki ta kasar Amurka, kuma tana fatan Amurka ta fahimci hanyoyin neman ci gaba da kasar Sin take amfani da su. Ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta kara fahimtarta game da babbar moriya da bukatun kasar Sin, tare da daidaita manufofinta kan kasar ta Sin, domin yin hadin gwiwa da ita wajen raya dangantakar dake tsakaninsu.
- Tsakanin Nijeriya Da BRICS+: Idan Zamani Ya Dinka Riga…
- Yaƙin Gaza: Falasɗinawa Sun Fara Neman ‘Yan Uwansu Da Suka Ɓace A Baraguzan Gine-gine
Cikin ‘yan shekarun nan, matakan kariyar ciniki da kimiyya da fasaha da kasar Amurka ta dauka a kan kasar Sin ba su hana samun bunkasur Sin ba. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kara ‘yancin kanta, da tsaro da kuma moriyarta ta neman samun bunkasa.
Yanzu dai, an bude wani sabon babin dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Idan kasashen biyu suka bi manufar diflomasiyya da shugabannin kasashen biyu suka kafa, wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma kamar yadda ake fata, tabbas, Sin da Amurka za su bude wani sabon babi mai kyau na kyautata dangantakarsu da shimfida sabuwar hanya mafi dacewa wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. (Mai Fassara: Maryam Yang)