Ana sa ran darajar kasuwar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI ta kasar Sin, ta kai dala biliyan 26.44 a shekarar 2026.
Wani rahoton kamfanin binciken harkokin kasuwanci na duniya (IDC), ya yi hasashen cewa, abun da za a kashe a kasuwar AI ta kasar Sin a shekarar 2023, zai kai dala biliyan 14.75, wanda ya dauki kaso 10 na jimilar ta duniya baki daya.
Da yake bayyana kyakkyawan fata game da fadadar kasuwar AI ta kasar Sin, rahoton na IDC ya jaddada muhimmancin kirkire-kirkire da daukaka fasahar AI, wajen kyautata aiwatar da abubuwan da ake muradi.
Ya kara da cewa, sha’awar masana’antu na komawa amfani da fasahohin zamani zai bunkasa bukatu a kasuwar kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp