Rahotanni daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin na cewa an gudanar da taron ministocin kudi na kungiyar APEC karo na 30, a ranaikun Lahadi da jiya Litinin a birnin San Francisco na kasar Amurka.
Game da hakan, ministan kudi na kasar Sin Lan Fo’an, ya bayyana cewa, yanayin farfadowar tattalin arzikin duniya a halin yanzu na tattare da matsaloli, kuma karfin tattalin arzikin yana raguwa, kana ana samun tabarbarewa a fannonin cinikayya da zuba jari, baya ga fuskantar wahalhalu a fannin neman ci gaba mai dorewa.
- Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Kasar Amurka Domin Gudanar Da Taron Shugabannin Kasashen Sin Da Amurka Da Taron APEC Karo Na 30
- CGTN: Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma A Bali Na Da Muhimmanci Wajen Inganta Alakar Sin Da Amurka
Jami’in ya kara da cewa, ya kamata dukkanin bangarori su karfafa hadin gwiwa ta fuskar manyan manufofi game da tattalin arziki, da inganta samar da ‘yanci, da saukaka fannin zuba jari, da kafa tsarin masana’antu mafi inganci a yankuna, tare da raya budadden tsarin tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pasific, da na duniya baki daya.
Tun daga farkon wannan shekarar, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da farfadowa da ingantuwa, musamman tun daga rubu’i na uku, kuma sauye-sauye masu kyau da ake samu na kara karuwa, kana ana kara azamar raya tattalin arziki. Don haka, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da farfadowa a cikin rubu’i na hudu. Har yanzu dai kasar Sin na kasancewa muhimmin ginshiki na ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)