• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Sa Ran Yankin Hong Kong Zai Samu Wani Sabon Ci Gaba A Cikin Shekaru Biyar Masu Zuwa

by CMG Hausa
3 years ago
Hong Kong

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Tun a lokacin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, shugaban kasar Xi Jinping ya nuna kulawa matuka game da wadata da zaman lafiyar yankin musamman na Hong Kong, da moriyar jama’ar wurin da walwalarsu, inda ya yi nuni da cewa, ci gaba shi ne ginshikin raya yankin Hong Kong da kuma magance matsaloli daban-daban.

Shin ta yaya yankin Hong Kong zai samu sabon ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa?
A wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin, wanda aka gudanar a jiya Jumma’a, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu dabaru 4 da yake fatan za su samar da ci gaban HK.

Dabarun hudu sun hada da “Mayar da hankali kan kara matsayin shugabanci” da “Kara karfin inganta ci gaba” da “Warware matsalolin da jama’a ke fuskanta “, da kuma “Wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare”.
Xi Jinping ya kuma bayyana fatan sabuwar gwamnatin yankin za ta aiwatar da manufar “kasa daya, mai tsarin mulki biyu” tare da gudanar da ayyuka masu amfani, da kuma mai da hankali kan warware batutuwan da suka fi damun mazauna Hong Kong.

Xi Jinping ya bayyana cike da kauna cewa: “A halin yanzu, abin da ya fi jan hankulan jama’ar Hong Kong shi ne, fatan samun rayuwa mafi kyau, da zama a cikin gida mai fadi, da samun karin damammakin raya sana’o’i, da samar da ilimi mai inganci ga yara, da kuma samun kulawa mai inganci idan an tsufa.” Don haka, ya bukaci sabuwar gwamnatin yankin da ta dauki bukatar al’umma, musamman ma fararen hula, a matsayin babbar manufarta ta gudanar da mulki.
Bisa la’akari da yadda ake matukar bukatar tsaro don samun ci gaba, shugaba Xi Jinping ya ce, bayan fuskantar tashin hankali, kowa yana jin cewa, Hong Kong ba zai kasance cikin rudani ba, kuma ba za a iya jinkirta ci gaban yankin ba. Yana mai cewa, dole ne a kawar da duk wani katsalandan tare da mai da hankali kan ci gabansa.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 
Daga Birnin Sin

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba
Daga Birnin Sin

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Next Post
An Gano Sama Da Yara 50 Da Aka Sace A Wani Cocin Ondo

An Gano Sama Da Yara 50 Da Aka Sace A Wani Cocin Ondo

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Gargaɗi, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Gargaɗi, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025
Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

October 22, 2025
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

October 22, 2025
Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

October 22, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.