An gudanar da taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) ta yanar gizo a ranar 18 ga wannan wata, inda bangarori daban daban suka cimma daidaito kan yadda za a gaggauta gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma a sabon zamani, da inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma kiyaye amfanin dandalin tattaunawar na FOCAC.
A shekarun baya-baya nan, bisa tsarin dandaloli irin su bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin, da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da kasashen Afirka, da bikin sayar da kayayyakin Afirka ta intanet, karin kayayyakin Afirka sun shiga kasuwar kasar Sin.
Alkaluman kididdiga na nuna cewa, tun bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a nan birnin Beijing a shekarar 2018, an ba da izinin shigar da kayayyakin amfanin gona da kayayyakin abinci iri 25 daga kasashen Afirka 14 da suka hada da kasashen Kenya, da Afirka ta Kudu, da Benin, da Masar zuwa kasar Sin. Kasar Sin ta kasance kasa ta biyu a duniya wajen sayen kayayyakin amfanin gonan kasashen Afirka.
A shekarar 2021, yawan kudin kayayyakin amfanin gona da kasashen Afirka suka sayar wa kasar Sin ya karu da kashi 18.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2020.
Ban da wannan kuma, tun bayan da aka kafa dandalin tattaunawar na FOCAC, tsawon hanyoyin jiragen kasa da kamfanonin Sin suka gina ko gyara a kasashen Afirka ya zarce kilomita dubu 10, tsawon hanyoyin motoci ya kai kimanin kilomita dubu 100, yawan gadoji ya kai kusan dubu daya, yayin da yawan tasoshin jiragen ruwa, ya kai kusan dari daya, da asibitoci da makarantu da dama, da samar da ayyukan yi fiye da miliyan 4 da dubu 500 a kasashen Afirka.
Jama’ar kasashen Afirka sun yaba matuka da wadannan nasarori. (Zainab)