Hukumomi na dab da sakar wa kamfanoni masu zaman kansu da kuma hukumomi a jihohi damar gudanar da jigilar aikin Hajji da Umara baki daya.
An dauki matakin ne bayan wani taro da kamfanonin gudanar da aikin Hajjin da masu zaman kansu suka gudanar a Abuja.
- An Gudanar Da Taron Wayewar Kai Ta Yanar Gizo Na Kasar Sin Na 2024 A Chengdu Na Sin
- Yawan Ribar Da Masana’Antu Masu Matsakaicin Kudin Shiga Suka Samu Ya Karu Da Kashi 3.6% A Farkon Watanni 7 Na Bana
Sun nuna suna son hukumar aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta bar musu aikin tafiyar da Hajji baki daya daga shekarar 2025.
Taron wanda kungiyar kamfanonin aikin Hajji da Umara masu zaman kansu ta Auhun ta gudanar a Abuja, ya fara ne da duba nasarori da kuma kalubalen da aka samu a Hajjin 2024.
Sannan ya tattauna kan yadda za a tabbatar da cewa su ne suka gudanar da aikin na 2025 baki daya.
Ikirama Muhammad, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar ta Auhun, ya shaida wa BBC Hausa, cewar suna da kwarin gwiwar za su inganta aikin.
A ranar 19 ga wannan watan Agusta ne Shugaba Bola Tinubu, ya sauke shugaban NAHCON, Jalal Arabi, yayin da hukumar EFCC ke tuhumar sa da yin almundahanar kudaden aikin Hajjin bana.
Tinubu ya maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban hukumar.