Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Graham Potter ya ce ya kadu tare da iyalansa, bayan samun sakon barazanar kisa, sakamakon da kungiyar ba ta kokari a karkashinsa.
Kungiyar ta ci wasanni biyu daga cikin 14 da ta buga baya a dukkan fafatawa, wadda a makon jiya Southampton ta doke ta a Premier League sai dai duk da haka shugabancin kungiyar na Chelsea ya sanar cewar tana goyon bayan Potter da iyalansa dari bisa dari tana tare da shi.
”Na karbi sakon wasika ta internet, wanda ke dauke da barazanar kisa ba sakone mai dauke da kalaman farin ciki da za ka karanta ba.” A cewar Graham Potter, dan asalin kasar Ingila.
Graham Potter ya zama kociyan Chelsea cikin watan Satumban shekarar da ta gabata, bayan da ta kori Thomas Tuchel – wasa tara Chelsea ta yi nasara daga 25 baya-bayan nan.
Chelsea tana ta 10 a teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da gurbin ‘yan Champions League da ke fatan buga wasannin badi sanann ranar Lahadi Chelsea ta buga wasan hamayya a gidan Tottenham a gasar Premier League mako na 25 inda ta yi rashin nasara da ci 2-0.