A jamhuriyar Nijar an samu ana musayar yawu bayan sanarwar kamfanin Orano, mai hakar ma’adanai dake cewa shi ya sayi jirgin shugaban kasar Nijar a shekarar 2014.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Hakan dai ya biyo bayan kwace lasisin hakar ma’adanin Uranium a daya daga cikin manyan cibiyoyi da ke arewacin kasar, daga hannun kamfanin.
- An Shiga Alhini A Nijar Bayan Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Sojoji 20
- An Kaddamar Da Ficewar Sojojin Amurka Daga Nijar A Hukumance
Sai dai a baya lokacin da ake kiran kamfanin Orano da sunan Areva, da kansa ya musanta batun da ke cewa ya bai wa gwamnatin Nijar din kudin sayen jirgin.
A shekarar 2015 ne gwamnatin Shugaba Muhammadou Issoufou ta sayi sabon jirgin shugaban kasa, tun daga lokacin takaddama ta barke kan hakan.
Batun ya janyo muhawara tsakanin wakilan majalisun Nijar, babban abin da ya janyo hakan kuwa yana da nasaba da batun masumagana da yawun masu rinjaye ya yi cewa za a sayi jirgin ne da kudin da aka samu daga kamfanin hakar ma’adinai na Areva wanda a yanzu aka sauya masa suna zuwa Orano.
To amma cikin gaggawa kamfanin Areva na kasar Faransa da bangaren gwamnatin Issoufou sun musanta hakan.
Shekara goma da yin wannan, bayan sojojin Nijar sun hambarar da mulkin Shugaba Muhammad Bazoum da ya gaji mulkin daga Muhammadou Issoufou, gwamnatin mulkin sojan suka sanar da karbe lasisin hakar ma’adinin Uranium daga Orano.
Shi ne kamfanin ya yi amai ya lashe tare da tabbatar da cewa da kudinsa aka sayi jirgin na shugaban kasa a zamanin mulkin Muhammadou Issoufou.