Ana zargin wani mahaifi, mai suna Confidence Amatobi da ke a yankin Amurie cikin karamar hukumar Isu a Jihar Imo, bisa karya hannun jaririnsa mai suna Miracle.
Amatobi ya dai dauki wannan danyen hukuncin ne a kan jaririn na a dan sati takwas da haihuwa saboda jaririn na damunsa da kuka idan yana barcin da daddare.
- Xi Ya Jaddada Aiwatar Da Muhimman Ka’idojin Babban Taron JKS A Cikin Rundunar Sojojin Kasar
- Rashin Tsaro: Amurka Ta Umarci Jami’anta Su Fice Daga Abuja
Mahaifin ya karya wa Miracle hannunsa ne, na dama ta hanyar rabka masa hanga ta roba da ake rataye kayan sanyawa don ya dakatar da jaririn daga kukan da yake yi, inda sakamakon rabka wa jaririn hangar, ta janyo aka cire masa hannun.
Mahifiyar jaririn tare da kungiyar mata ‘yan jarida (NAWOJ) reshen jihar da hukumar kare ‘yancin bil Adama ta kasa (NHRC) suka yi kira ga gwamnatin jihar da rundunar ‘yansandan jihar da su gaggauta cafke Amatobi tare da hukunta shi.
Shugabar NAWOJ reshen jihar, Dakta Dorothy Nnaj a hirarta da ‘yan jarida a garin Owerri a lokacin da ta je asibitin gwamnatin tarayya da aka kwantar da jaririn ta yi zargin cewa, kwada wa jaririn hangar, ya janyo an cire masa hannun dama.
Dakta Dorothy, ta kuma nuna takaicinta kan yadda mahaifin ya ci zarfin jaririn da matarsa ta haifa masa saboda kawai, kukan jaririn na hana shi barcin dare.