Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya.
Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi.
Ta ce, nan da shekaru 25 masu zuwa, mutane kusan miliayn 800 na kasashen Afirka da na Latin Amurka za su yi kaura zuwa birane, kuma kasashen Asiya da dama su ma suna fuskantar kalubalen fama da talauci. A cewarta, birane na da muhimmanci sosai wajen kawar da talauci, kuma ba ma kawai ya kamata a ba da wurin kwana ga mutane a cikin birane ba, har ma ya dace a ba su damammakin samun ilmi, da guraben ayyukan yi da sauransu, da kuma samun hidimomin kiwon lafiya don kiyaye koshin lafiyarsu, kana ta ce, wannan shi ne muhimmin abun da za mu ci gaba da gudanarwa da kuma tattaunawa a kai. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp