Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare.
Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi.
Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa ga kololuwar fitar da sinadarin carbon a kasar Sin kafin shekarar 2030, wanda tuni aka cimma nasararsa. Har wa yau, yayin da kasashe da dama ke tunanin dabarun kyautata motoci dake aiki da man diesel, tun shekaru da dama da suka wuce kasar Sin ta kuduri aniyar kara raya kirar motoci dake aiki da lantarki, kuma a halin yanzu irin wadannan motocin na mamaye kasuwannin dukkanin fadin duniya.
Guterres ya kuma ce, yayin da duniyarmu ke fuskantar tarin yanayin rashin tabbas, abu ne mai wuya a iya tsara manufofi masu dorewa, don haka, sanin ya kamata da shugaba Xi ke da shi wajen tsara manufofi na da matukar muhimmanci. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp