Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi na’am da shawarar inganta jagorancin duniya ko GGI, da kasar Sin ta gabatar a farkon makon nan, yayin taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko (SCO Plus).
Kakakinsa Stephane Dujarric ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, inda ya ce mista Guterres ya bayyana shawarar a matsayin muhimmin mataki na kare tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa karkashin MDD, dake zama jigon cimma nasarar hakan.
Kakakin ya ce mista Guterres ya yi tsokacin ne yayin da ya halarci taron koli na SCO a birnin Tianjin a arewacin kasar Sin a ranar Litinin, yana mai bayyana shawarar ta GGI a matsayin jigon ingiza tsarin cudanyar sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp