Dan wasan gaba na Manchester United, Antony zai iya buga wasan da Manchester United zata fafata da Galatasaray a gobe Talata 2 ga watan Oktoba.
Dan wasan na Brazil bai buga wasa ba tun farkon watan Satumba bayan da aka zarge shi da cin zarafin tsohuwar budurwar sa.
- Newcastle Ta Kori Manchester City A Gasar League Cup Ta Kasar Ingila
- Chelsea Ta Nuna Sha’awar Daukar Matashin Dan Kwallon Arsenal
Antony, wanda ya musanta zargin, ba a kama shi ba ko kuma a tuhume shi a duka kasashen biyu Brazil da Birtaniya sai dai ya bawa jami’an tsaro hadin kai wajen bincike.
A ranar Lahadi dan wasan ya koma daukar horo a kungiyar kuma kociyan Man Utd Erik ten Hag ya ce watakila Antony ya buga wasan da zasu kece raini da Galatassary a gasar kofin zakarun turai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp