Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna na adawa da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Uba Sani na jam’iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar.
- Sabon Gwamnan Zamfara Ya Lashi Takobin Magance Matsalolin Da Suka Addabi Jihar
- Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Dawo Da Taimakon Kudin Da Ake Baiwa Sudan Ba Tare Da Wani Sharadi Ba
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Felix Hyet a ranar Talata ya yi watsi da sakamakon da jami’in zaben, Farfesa Lawal Bilbis ya sanar.
Hyet ya lura cewa Sanata Sani ya samu kuri’u 730,002 inda Ashiru ya samu kuri’u 719,196.
“PDP ba ta amince da wannan sakamako ba. Mun yi watsi da ikirarin da INEC ta yi na cewa Uba Sani ya lashe zaben gwamna,” in ji shi.
Jam’iyyar adawar ta yaba wa ‘yan jam’iyyar da magoya bayanta bisa goyon bayan da suka bayar, inda ta sha alwashin kwato hakkinta.
Hyet ya bayyana shirye-shirye don kalubalantar sakamakon zaben bisa tsarin doka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp