Jam’iyyar APC a Jihar Kano, ta bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wa’adin kwanaki bakwai don sake duba sakamakon zaben gwamnan jihar.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa jami’in zaben Kano, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Magoya Bayan Peter Obi Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Abuja Kan Zaben 2023
- Zan Yi Salon Mulki Irin Na Kwankwaso —Abba Gida-Gida
Ya jingina wannan furucin ne a kan fassarar da ya yi wa dokar zabe da kuma ka’idojin zabe cewa inda aka soke zabe sakamakon tashin hankali a kidaya tazarar shugabanci tsakanin na farko da wanda ya zo na biyu ba.
Sai dai a jawabin da jam’iyyar ta yi a taron manema labarai a ranar Talata, ta bakin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na jihar, Barista Abdul Fagge, ta ce jami’in hukumar zabe ta INEC ya yi kurakurai tare da yin zagon kasa ga dokar zabe ta hanyar bambance soke-soke saboda tashin hankali da wuce gona da iri.
Fagge ya ce an tattara katunan zabe 273,442 a wuraren da aka soke zaben sakamakon tashin hankali da kuma yawan kuri’u, adadin da ya ce ya nuna cewa tazarar (128,897) da aka yi amfani da ita wajen bayyana Yusuf na NNPP bai wadatar ba bisa ga dokar zabe.
Ya ce, abin mamaki ne a ce da zaben guda 16 na ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar a rana guda kuma a karkashin sharuddan da INEC ta ce ba a kammala ba.
A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya ce INEC ba ta bi sharuddan da ta yi amfani da su wajen bayyana sakamakon zaben mazabarsa na tarayya a matsayin wanda bai kammala ba.
Shi ma da yake jawabi, dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar, Nasir Yusuf Gawuna, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da kwantar da hankulan jama’a, tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu.
Gawuna, mataimakin gwamnan jihar, ya bayyana fatansa na cewa INEC za ta yi abin da ya kamata.