Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya burge kwamitin tantance jam’iyyar APC na Cif John Odigie Oyegun.
Kwamitin da ke tantance ‘yan takara 23 da ke neman zama shugaban kasar Nijeriya a karkashin jam’iyyar APC na gudanar da tantance ‘yan takara a Otel Transcorp Hilton Abuja.
- 2023: Jm’iyyar APC Ta Fara Tantance Masu Neman Takarar Shugabancin Nijeriya
- Ina Fata Deliget Ku Zabe Ni Ranar Zaben Fitar Da Gwani Ko Ban Baku Ko Sisi Ba —Badaru
A cewar Daraktan, Yada labarai da Sadarwa na kwamatin kamfen dinsa, Bayo Onanuga, ya ce kwamitin ya gamsu da yadda Tinubu ya amsa tare da bayar da karin haske kan yawancin tambayoyin da aka yi masa.
Ya ce wasu daga cikin tambayoyin sun shafi tarbiyyar sa da iliminsa da sana’a.
“Ya shaidawa kwamitin da kwarin guiwa dalilin da ya sa ya cancanci ya jagoranci Jan ragamar jam’iyyar APC a matsayin dan takararta na shugaban kasa. Ya ba da misali da nasarar da ya samu a matsayinsa na gwamnan jihar Legas, inda ya kara samar da kudaden shiga na cikin gida daga N600m a duk wata, wanda a yanzu ya karu zuwa N51bn a yau.
“Ya kuma ba da misalin gayyatarsa ga Enron don fara samar da wutar lantarki ta farko a Nijeriya ,” in ji shi.
Tsohon manajan daraktan Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya kara da cewa kwamitin tantancewar ya bayyana gamsuwa da sanin Tinubu kan harkokin tattalin arziki da zamantakewa da siyasa da ke addabar kasar.