An ayyana Mista Saleh Zock na jam’iyyar (APC) a matsayin wanda ne ya lashe zaben mazabar dan majalisar tarayya ta mazabar Kachia/Kagarko da aka gudanar ranar Asabar.
Jami’in kula da zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Haruna Aminu na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya ne ya sanar da sakamakon zaben ranar Litinin a Kaduna.
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Kakakin Majalisar Kaduna
- LP Ta Lashe Zaɓen Mazaɓar Ɗan Majalisar Tarayya Ta Jos North/Bassa A Zaɓen Cike-gurbi
Aminu ya ce Saleh Zock na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 42,461 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Umar David na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 26,218.
Ya ce Augustine Umar na jam’iyyar Labour (LP) shi ne ya zo na uku da yawan kuri’u 2,311.
An gudanar da zaben ne a mazabu shida da suka shafi kananan hukumomi bakwai da suka hada da Chikun da Igabi da Kaduna ta Kudu da Kudan da Kachia da Kagarko da kuma Kauru.
Jimillar rumfunan zabe a mazabun sun kai 1,114, yayin da wadanda aka yi wa rajista a wurin suka haura 639,914.