Jam’iyyar APC ta nemi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta soke zaɓen cike gurbi da ake yi a mazaɓar Shanono/Bagwai da kuma zaɓen mazaɓar Ghari saboda tashin hankali.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya sanya hannu, APC ta ce ‘yan daba ɗauke da makamai sun kai farmaki a rumfunan zaɓe da dama a Shanono, Bagwai da Ghari.
- Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa
- Zaɓen Cike Gurbi: DSS Ta Kama Wani Jam’in Jam’iyya Da Maƙudan Kuɗaɗe A Kaduna
Hakan ya sa masu kaɗa ƙuri’a suka gudu yayin da jami’an tsaro suka kasa shawo kan lamarin.
“Rahotanni sun nuna cewa masu zaɓe sun tsere, jami’an tsaro kuma sun gagara shawo kan lamarin. A irin wannan yanayi, yin sahihin zaɓe mai inganci ba zai yiwu ba,” in ji sanarwar APC.
Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa ci gaba da gudanar da irin wannan zaɓe zai ƙara ƙarfafa maguɗi da tashin hankali.
“Ci gaba da zaɓen cikin barazana da tsoratar da masu zaɓe ya saɓa wa dimokuraɗiyya da adalci,” in ji Morka.
APC ta buƙaci INEC da ta soke zaɓen nan take domin kare jama’a da kuma tabbatar da sahihi sakamako.
Har yanzu, INEC ba ta mayar da martani kan wannan buƙata ba.
Ana ci gaba da samun tashin hankali a yankunan da abin ya shafa, yayin da ƙungiyoyi da masu sa ido kan zaɓe ke bibiyar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp