Jam’iyyar APC a Jihar Edo ta yi gargaɗin cewa duk wani kwamishina da ya halarci taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC meeting) ba tare da sanya hular Tinubu ba, zai fuskanci dakatarwa daga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Emperor Jarrett Tenebe, ya bayyana haka a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, inda ya ce rashin bin wannan umarni na gwamna Monday Okpebholo alama ce ta rashin ladabi da rashin biyayya ga shugabanci.
- Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
- Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro
A baya-bayan nan, gwamna Okpebholo ya umarci kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati su kasance suna sanya hular Tinubu a lokacin taron majalisar zartarwa domin nuna goyon baya da biyayya ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da jam’iyyar APC.
Tenebe ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na shirye-shiryen jam’iyyar don tabbatar da cewa APC ta samu ƙuri’u miliyan 3.5 ga Shugaba Tinubu a zaɓen shekara ta 2027, yana mai jaddada cewa duk wanda bai amince da wannan tsarin ba, ba cikakken ɗan jam’iyyar bane.
“Mun bayyana biyayyar mu ga Shugaban ƙasa ta hanyar sanya hular Tinubu,” in ji shi. “Waɗanda ke kuka kan wannan doka ba ‘yan APC na gaskiya ba ne. Mun riga mun bayyana a nan Edo — babu hular Asiwaju, babu shiga majalisar zartarwa.”













