Jam’iyyar APC ta sanar da cewa za ta gudanar da babban taronta na ƙasa tsakanin Laraba, 25 zuwa Asabar, 28 ga Maris, 2026.
APC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakatarenta na Ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya sanya wa hannu kuma ya wallafa a shafin jam’iyyar na X a hukumance a ranar Lahadi.
- Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey
- Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN
Basiru ya bayyana cewa sanarwar ta yi daidai da tanadin Sashe na 11: A ƙaramin sashe (i-xi), da Sashe na 17(0) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
A cewar sanarwar, za a gudanar da taron ƙananan hukumomi da na unguwanni na jam’iyyar mai mulki a ranakun 18 da 20 ga Fabrairu, 2026, bi da bi.
Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa ya ƙara da cewa rajistar ‘ya’yan jam’iyyar ta hanyar intanet, wacce aka fara a ranar 1 ga Disamba, 2025, zai ƙare a ranar 30 ga Janairu, 2026.














