Kungiyar masu kula da sana’ar POS ta bayyana aniyarta na daƙile haramtacciyar hada-hada a sana’ar. Shugaban Kwamitin Amintattun Kungiyar na Kasa, Barista Ibrahim Abdullahi Gurin, shi ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa dake Abuja.
Ya ce, kungiyar na nan tana aiki yadda ya kamata a wannan tsari da ake ciki na dijital, kuma tana ci gaba da rajistar mambobinsu a kan manhajar kungiyar domin sanin adadin mambobinsu, tare da ci gaba da ganin ofisoshinsu na jihohi da na kananan hukumomi sun kafu kuma suna aiki yadda ya kamata, wanda hakan shi zai ba su damar ganin sun tunkari yawan masu amfani da POS a fadin kasar nan.
- Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya
- NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji
Game da masu haramtacciyar hada-hada ko biyan kudin fansar wadanda aka yi garkuwa da su, Gurin ya ce, tun da aka kafa wannan ƙungiya da wannan hali suke fada. A cewarsa, “Daga shekara biyu zuwa yanzu, waɗannan abubuwa sun ragu sosai saboda mun yi tsayin daka wajen wayar da kan jama’a illar abun, don haka mun taka muhimmiyar rawa wajen ganin mun daƙile kaso mai yawa na wannan haramtacciyar hada-hadar.
Ya ci gaba da cewa, “an kama masu laifuka da dama ta hanyar bayanai da muke bai wa jami’an tsaro wanda hakan ya taimaka sosai wajen magance aikata laifuka a POS”, domin a cewarsa “sun sanya tsauraran matakai yadda ko da an tura kudi kafin a zo karɓa mambobinmu suna ganewa idan an tura kudin ta hanyar da ya dace, idan ba su gamsu ba sai a sanar da jami’an tsaro a zo a kama mutum, an kama wasu a Abuja, an kama wasu a Maiduguri da wasu sassa na kasar nan”.
Ya bayyana kungiyar a matsayin mai farin jini, inda ya ce dukkan jami’an Nijeriya sun santa kuma sun yi marhaban da ita ta hanyar kai musu ziyara gami da samun goyon bayansu.
Ya ce ba ma a nan kasar ba har da wasu kasashen waje idan akwai wata matsala da shafi wannan bangare, jami’an tsaron kasar su kan tuntube su. A fannin inganta kanana da matsakaitan sana’o’i kuwa, ya ce kungiyar na yin duk mai yiwuwa wajen ganin mambobinta sun ci gajiyar shirin da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa.














