A daidai lokacin da Musulmi fiye da Miliyan 1.5 suka halarci Arafat a ci gaba da ayyukan Hajjin bana, Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta jagoranci gabatar da adduo’i na musamman ga kasa Nijeriya.
Taron ya samu halartar manyan Malaman addinin musulunci daga sassan Nijeriya.
- Cibiyar Noma Za Ta Samar Da Ingantaccen Irin Farin WakeÂ
- Garambawul Da Nijeriya Ke Bukata A Kan Shugabanci Da Zabe – ‘Yan Majalisa 30
Bayan jawabin maraba ga wadanda suka samu halartar taron, Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ya mika godiya ga dukkan wadanda suka bayar da gudummawar samun nasarar da aka yi a jigilar Alhazan bana, ya kuma nemi karin goyon baya don samun nasarar komawa da Alhazan mu gida.
An dai gabatar da adduo’i da yaren Ingilishi, Hausa, Yoruba, Ibo da Fullanci, Kanuri da kuma Nupe.
A cikin addu’o’in sun nemi Allah ya kara wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu basirar tafiyar da tattalin arzikin kasa. Sun kuma yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen ayyukan ta’addanci a sassan kasar nan.