Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta koma matsayi na daya akan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila, bayan ta doke abokiyar karawarta Brentford da ci 2-1 a filin wasa na Emirates.
Declan Rice ya zura wa Arsenal kwallo a minti na 19 da fara wasan, bayan da Ben White ya bugo masa wata kwallo daga gefen fili shi kuma yasa mata kai ta fada.
- Arsenal Na Ci Gaba Da Jan Zarenta A Gasar Firimiya Bayan Doke Sheffield Da Ci 6
- Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Manchester United Da Manchester City
Gab da tafiya hutun rabin lokaci Yoane Wissa ya farkewa Brentford kwallon da aka jefa masu bayan da mai tsaron ragar Arsenal Aron Ramsdale ya yi jinkiri wajen fitar da kwallon daga da’irarsa.
Wannan nasara da Arsenal ta samu yasa ta dare matsayi na daya a kan teburin gasar ta Firimiya da maki 64, inda Liverpool ke biye da ita da maki 63, sai Manchester City mai maki 62.