Arsenal ta doke Man Utd a ranar Lahadi inda ta kai maki 50 bayan wasanni 19 kacal – tarihin da Arsene Wenger ya kusa kafawa a shekarar 2003-04 amma bai yi nasara ba.
Arsenal ta kafa tarihi bayan da ta doke Manchester United da ci 3-2 a ranar Lahadi.
Arsenal ta kafa tarihin ne inda ta samu nasarar cin wasannin 16 a gasar ta bana kuma ta sami maki 50 a rabin matakin gasar ta Firimiya – Kungiyar Arsenal bata taba samun wannan tarihin ba a baya.
Ko lokacin onbitin (unbeaten) na 2003-04 da kungiyar tayi ta samun nasara a karkashin jagorancin Arsene Wenger, maki 45 kawai ta samu a wasanni 19.
Wannan tarihin, shine matakin da Arsenal ke kafawa a halin yanzu karkashin Mikel Arteta.